Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da takwas


Sayyed Zakzaky2

Ko ya halatta mutum ya karanta sura mai ayar sujada a salla?
TAMBAYA: Malam mutum ne yake kallo na kafiri, amma ni ina yi masa kallon musulmi, ko zan iya bin sa salla?

SHAIKH ZAKZAKY: Tunda kai ba kai ne kake kallonsa kafiri din ba, ai kai ba ka da matsala da shi, shi ne yake da matsala. Saboda haka kai dai yadda kake ganin sa din nan haka za ka kalle shi. Kuma dai wancan matsalarsa ce, ba taka ba.


TAMBAYA: Malam menene hakkin mace a kan mijinta a Musulunci?

Daga Maryam Sani Benin Nijeriya 0802 704 3450

SHAIKH ZAKZAKY: Mun sha cewa in tambaya ta cika zama a dunkule takan yi wahalar amsawa, don yanzu ka ga ana so in kawo hakkoki kenan. Sai mu ce hakkoki suna da yawa. Kuma kamar yadda a dunkule Allah (T) ya ce 'walahunna mislul lazi alaihunna bil'amaruf,' ya nuna hakkokin, ba hakkin mace ne a kan miji kawai ba. Har ila yau ya nuna akwai hakkin miji a kan mace, kuma hakkin da ke kan wannan, shi ne ke kan wannan. Wanda kuma yake a kan wannan shi ne a kan wannan. A takaice daga cikin hakkokinta akwai zai dauki infakinta. Infaki kuma ya hada da wurin kwana da sutura da sauran dawainiyoyi na mutum, na tilas, da sauran hakkoki. Amma dai wannan da yake kamar yadda na ce, tambayar ta cika dunkulewa, kan sa da a ce ainihin wata mishkila ce aka tambaya ba wai a dunkule haka ba. A dunkule, sai dai kawai mu ce a je a duba babin aure, za a ga hakkoki.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko ya halatta mutum ya karanta sura mai ayar sujada a salla? Idan kuma mutum yana limanci, ko kuwa yana bin salla, sai Limamin da yake bi ya karanta, ya zai yi kenan?

Daga Khalidi Rijiyar Lemo Kano 0802 881 0135

SHAIKH ZAKZAKY: To an hana karanta sura mai sujada a sallar farali, amma babu laifi da karantawa a nafila. Saboda haka idan mutum ya karanta a sallar nafila, to, babu laifi ya yi sujada din. Amma in a farali ne, to tun farko kar ya karanta sura mai sujada, in ko har ya karanta, to, dole ya yi sujadar, kuma salla ta baci. Amma idan yana bin wani Liman, wanda yake a mazhabarsa shi ana iya karantawa, tunda ya halatta a bi Limami bisa sabanin mazhaba, idan mutum ya bi shi zai iya bin sa har ma ya yi sujadar, kuma babu laifi gare shi, tunda a wajen shi Limamin ta inganta.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ni dai Tela ne akan kawo min dinki, sai a ba ni a ce 'express' ne, sai mutum ya biya ni kudi mai yawa in yi masa. Ya matsayin wannan yake a Musulunci?

Daga Yahya Haruna Kaduna Road Suleja Neja 0803 641 2729

SHAIKH ZAKZAKY: In dai ba hakkin wasu ne za ka tauye ba, kamar alal misali sakamakon yin 'express' din za ka fasa wasu alkawura da ka daddauka na yi wa wasu a kan lokaci, ka fasa don ka yi 'express' din, zai zama babu laifi. Saboda wannan in za a yi da gaggawa ne, saboda haka za ka dauki wasu lokuta naka, kila ma har da ma lokacin hutunka, ka aje hutun don ka biya bukatar mai 'express'. Saboda haka a kan wannan ka caje shi fiye da idan da zai jira. A takaice in ba hakkin wani aka ci ba, zai zama babu laifi. Amma in ya yi 'express' din ya kai ma ga ya ci hakkin wani, to, zai zama da laifi. Kamar a fasa cika wa wani alkwari, don shi a cika masa nasa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ko ya halatta mace mai aure ta yi aikin gwamnati?

Daga Abubakar Alaba Internatiolan Market Legas 0803 330 6456

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da ya halatta wa namiji, yana da aure, ko ba shi aure ya yi aiki, shi ne kuma har ila yau zai halatta wa mace, tana da aure ko ba da ta aure. Wato ba wata danganta tsakanin aikin da batun aurenta, kuma ko na gwamnati ne, ko ba na gwamnati ba. Abin da za a yi la'akari da shi kawai shi ne, halas da haram a bayyane ne. In abin da take yi halas ne kuma bisa tsari wanda yake ya dace da shari'a, babu laifi da shi. A takaice babu wani bambanci tsakanin aurenta, ko rashin aurenta kan batun aiki, kuma na gwamnati ne, ko ba na gwamnati ba. Saboda haram da halas a bayyane suke.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam menene hukuncin ma'aikacin da wurin aikinsa ya kai nisan yin kasaru daga inda yake zaune?

Daga Sabo ATC Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: Matukar yana da gida daya ne inda yake zaune, can kuma yana zuwa wajen aiki ne. Yayin da yake tafiya da dawowa yana da hukuncin matafiyi ne. Sai dai a inda yake zuwa can aikin in yana da wani gida da iyalinsa, to, zai iya zama mai gida biyu, zai zama sai in yana kan hanya ne, in ya kai ma nisan yin kasaru zai kasarta, amma idan ya je can sai ya zama mazauni.

TAMBAYA: Malam ni matafiye ne ina zuwa Kudancin kasar nan, zan iya cin kowane abinci?

Daga Muhammad Sani Benin Nijeriya 0802 704 3450

SHAIKH ZAKZAKY: To a Kudu ko a Arewa, ko ma ina ne, halas bayyananne ne, haram bayyananne ne. Haram ba zai taba zama kamar halas ba, don ka je wani wuri. Saboda haka abin da duk za ka ci dole ka tabbatar da halascinsa, a ka'idar shari'a kafin ka ci. Kana Kudu ne, ko kana Arewa.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halatta musulmi ya ci yankan Ahlul Kitabi da muke da su a nan Nijeriya?

Daga Gambo Buhari gambobuhariradda@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: To, lalle ban san su waye Ahlul Kitabi a nan Nijeriya ba. Amma dai abin da muka sani shi ne, ba zai halatta ka ci yankan wani ba, sai na musulmi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Shin ko ya halatta mutumin da bai san hakikanin yadda ake yin aikin hajji ba a Imamiyyance ya tafi ya yi abin da ya sani, sannan a bangaren da bai fahimta ba, ya yi aiki da fatawar wata mazhabar ta daban?

Daga Mikaeel Abubakar Adam Suleja, jihar Nejr. majafariyya@yahoo.co.uk

SHAIKH ZAKZAKY: Laziminsa ne ya nemi sanin yadda zai yi aikin hajji din ma kafin ya tafi. Wajibinsa ne. Sannan kuma tilas ne ya yi aikin hajji din bisa ka'ida shimfidaddiya a bisa fatawowin Mujtahidin da yake taklidi da shi. In har kuma ya yi hajji din ba ta haka nan ba, to, wanda ya inganta a bisa ka'idar taklidinsa ya yi, wanda kuma bai inganta bisa taklidinsa, to, bai inganta din ba. Tana iya yiwuwa ma gaba daya hajjin bai yi ba, sai ya sake kenan. Sai ya duba ya gani bayan ya gama hajjin, wannene ya yi daidai, in ta kai ma ma hajjin ne ya rushe, to ya rushe din.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah Ya gafarta Malam, ina hukuncin zama da kanwar mata a gida daya wacce yake ta balaga? Mutum zai iya ganin ta, ba tare da hijabi ba?

SHAIKH ZAKZAKY: Wadanda za a iya ganin su ba tare da hijabi ba, ai ayyanannu ne, ciki kuma babu 'yar uwar mace. 'Yar uwar mace, na'am, muharramarka ce, haramci wanda ya takaita da zamani, wato matukar kana auren 'yar uwarta, ita ta haramta. Amma ba a ce za ka iya ganin ta ba tare da hijabi ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya yi tsintuwa ya sayar da tsintuwar ya yi amfani da kudin saboda a lokacin yana cikin hali na rashin abinci ga iyalinsa. Shin in ya sami kudin zai sake sayo abin tsintuwar ne ya nemi mai shi, ko kuwa ya zai yi?

Daga Abu Rulha Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To yanzu dai wannan abin da ya tsinta din yana nan a kansa ana bin sa bashi, saboda haka duk ran da mai wannan abin ya zo, to, dole shi zai biya shi. In ya halakar, ya biya shi kimarsa. Har kuma idan sam ba a sami mai abin ba, duk da haka nan dai ana bin sa bashi, ba a ce shi ya yi amfani da shi kawai ba, sai in abin bai taka kara ya karya ba, amma in ya kai wani mikidari na dukiya tilas ne hakkin wancan ne, sai dai ya yi masa sadaka da shi fisabilillahi, da fatan shi ya samu ladan. Kuma duk ran da ya zo yana bidar abinsa, to lalle tilashinsa ya ba shi. Wato dai a takaice shi yanzu bashi ne a kansa.

TAMBAYA: Malam ni dan acaba ne, na sayi mai mai araha na zuba a mashin dina ina aiki, sai kuma daga bisani mai ya yi wuya a gari, sai sauran abokan aikina suka kara kudin da suke daukar mutane zuwa wasu wurare. Ko ya halatta ni ma in kara?

Daga Abubakar Aliyu Likoro jihar Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle idan farashin abu ya karu ana la'akari da halin da yake a kasuwa ne a yanzu, ba a la'akari da yadda aka sayo shi da. Saboda haka canzawar kasuwa idan ka sai abu da araha, misali, sai kasuwarsa ta sake ya koma yana da tsada, to sabon kudinsa na yanzu ne za ka sai da shi, domin in ka je saye da sabon kudin za ka sayo. Kamar yanzu misali yana ganin cewa, ai ya sai mai mai araha ne a da, amma yanzu in ya koma zai sai mai din ai mai tsadar zai saya, kuma da wannan kudin da ya caza na aikin da aka biya shi zai sai sabon farashin mai don ya yi wani aiki. Saboda haka yanzu dai a takaice abin da za mu ce masa a wajen canzawar kasuwa, kullum akan yi la'akari da farashin da yake yanzu ne. Ba a kwatanta kowane abu da yadda yake a da don sai da shi a tsohon farashi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wani Malami yana cewa idan mutum ya kamu da ciwon kanjamau, sannan ya tuba daga zina, wai Allah ba zai yafe masa ba saboda yanzu ya san cewa mutuwa zai yi. Shin Malam haka abin yake?

Daga Adamu Abdullahi Kwadan Gombe adamukwadan@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle ba haka bane. Allah yana karbar tubar mutum matukar bai kai gargara ba, wato da a ce ya kai gargara ya ga yana gargarar mutuwa din ne, ya tuba, tuban ba zai amfane shi ba. Amma don mutum yana ciwon ajali ba a ce ai ya kai gargara bane, ballantana cowon da ma tana iya yiwuwa ma a warke.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam na yi tafiya ne zuwa Zariya, sai lokacin salla ya same ni a can, amma ban yi ba, sai da na zo kusa da Kano sai na tuna, sai na yi kasaru, a wannan lokacin kasarun da na yi ta isar min, ko kuwa sai na cika sallar bayan kasarun da na yi?

Daga Musa El-Husain Kurna T/Fulani Kano musahsn@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: To tunda bai ce ya shiga Kano bane, ya ce kusa ne, sai mu ce idan muhallin da ya yi salla din ya kamata ya cika ne, to, lalle cikawa zai yi, sannan kuma a tafuskacin 'ihtiyadi' sai kuma ya sake kasaru. Amma tunda ya ce mana kusa ne, tana iya yiwuwa har yanzu yana muhallin kasuru ne, saboda haka kasarun kawai zai yi dama, in ma har ma ya cika, dole sai ya sake kasaru. Amma tunda yake kusa ne ban san wannene ba. Ana cewa mafarar kasaru shi ne makararsa, kuma yana farawa ne bayan an bar gari, yana karewa bayan an shigo gari. A da can akwai ganuwa na gari wanda akan ce in ka je ganuwar gari shi kenan. Amma yanzu saboda garin ya wurwuce ganuwa, saboda haka za mu iya cewa in dai yanzu da za a tambayi mutum a ce yanzu ka shiga gari kaza? Idan amsa eh ne, to daga nan kasaru ta yanke. In kuma amsa a'a ne, bai shiga bane, to yana nan zai yi kasaru. Saboda haka tunda ya ce mana kusa ne, in dai bai shiga Kano ba, to yana nan a muhallin kasaru, in kuwa har ya shiga cikin garin Kano, amma bai isa gidansu ba, to kasaru ta fadi a kansa, saboda haka yanzu zai cika salla ne, ya kuma biya kasarun da ta kama shi ta fuskacin 'ihtiyadi.'

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin wanda bai yarda da Musuluncin wasu ba, har ma yana wulkanta su yana ci masu mutunci?

Daga Mahammadu Sani Rimin Kaura jihar Katsina mulsaf4luv@yaho.com

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle shi Musulunci wani abu ne sananne. Mai shaidawa da la'ilaha illallah sunansa musulmi. Ba a ce kana yarda ne, ko kuwa rashin yarda da Musuluncinsu ba, saboda ainihin Musuluncinsu, wani abu ne wanda yake Allah ne kadai ya iya yi masu hukunci dangane da shi. Kai zahiri za ka yi amfani da; idan zahiri mutumin nan yana ayyuka da sunansa Musulmi ne, to a musulmin za ka yi mu'amala da shi, saboda haka zai zama haramun ne ga musulmi ya dauki wani musulmi a matsayin wai shi bai aminta da Musuluncinsa ba, tunda ba wanda aka kallafa maka hukuncin aminta ko rashin aminta da Musuluncinsa. Tunda hukuncin imaninsa ba shi a hannunka, za ka yi amfani da zahiri ne, kuma Allah (T) shi ne mai wannan hukuncin, kuma bai dora maka.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah ya gafarta Malam, menene yake sa musulmi ya ji ba ya so ya yi salla a kan lokacinta. Sannan menene ya kamata idan mutum ya samu kansa a kan irin wannan hali ya yi?

Daga Usman Muhammad usbogon@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: Ina ganin raunin imani ne. Saboda haka sai ya yi kokari ya tsoratar da ransa azabar wuta. Kuma in ya ji duk bai tsorata ba, to ya kwadaitar da ita dadin Aljanna. Ya tsoratar da kansa kuma mutuwa, wanda tana iya zuwa masa kowane lokaci. Kuma ya karanta babin tsawatawa kan sakaci da salla, ya ji irin azabar da aka yi tanadi ga wanda yake sake da ita. Mai yiwuwa irin wadannan zai iya kara masa karfin imani ya zabura.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Lamborghini Huracán LP 610-4 t